Monday 19 January 2026 - 22:29
Alaƙar Fiƙhu da Akhlaƙ

Hauza/Shugaban Makarantun Hauza a taron kasa na Fiƙhu da Akhlaƙ, ya gudanar da bitar alaƙar dake tsakanin Fiƙhu da Akhlaƙ inda ya tabbatar da bukatar sake dubawa da nazarin wannan alaƙa.

A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, Ayatullah Alireza A'arafi, Shugaban Makarantun Hauza na Iran, a taron kasa kan Fiƙhu da Akhlaƙ da aka gabatar a Jami'ar Ƙur'ani da Hadisi, ya gudanar da bitar alaƙar tsakanin Fiƙhu da Akhlaƙ inda ya tabbatar da bukatar sake dubawa da nazartar alaƙar.

Shugaban Makarantun Hauzar da farko ya yi bayani kan cika shekaru dubu da dari biyar (1500) da haihuwar Manzon Rahama (SAWA) da kuma shawarar jagoran juyin juya halin Musulunci kan riko da Nahjul Balagha, inda ya karanta wani bangare na huduba ta 94 da take bayani kan siffofin Annabin Rahama (S).

Ayatullah A'arafi, a ci gaba da bitar alaƙar dake tsakanin Fiƙhu da Akhlaƙ, ya ce: "Ta iya yiwuwa mutum ya kalli Kalam da Fiƙhu a matsayin mabanbanta, amma yana iya cewa su din a tare da juna sun samar da fiffiken wani tsari ne guda daya. Siffofin Akhlak zasu iya zama maudu'in hukunce-hukuncen Fiƙhu, sannan kuma dole ne Fiƙhu ya iya yin bayani akan bangarori daban-daban na dan adamtaka."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha